Labarai

Mijina ya gargaɗi ni yace bazai iya biyan kudi ba idan naka sace ni- matar El-Rufa’i Hadiza

Uwar gidan gwamnan Kaduna takai ziyara gonar ta inda ya jaddada aniyar gwamnatin jihar na ba zata biya kuɗin fansa ba
– Hajiya Hadiza Elrufa’i ta ce tun kafin ta fito mijin nata ya gargaɗe ta da cewa ba zai biya ko sisi ba da sunan kuɗin fansa idan aka sace ta
– Har yanzun dai ɗalibai 39 na hannun yan bindiga, kuma sun nemi a biya su 500 miliyan kafin su sake su
Uwargidan gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Hadiza malam Nasir Elrufa’i ta kai ziyara gonar ta, ta kuma ce mijinta ya faɗa mata ba maganar biyan kuɗin fansa idan aka sace ni.
Hadiza El-rufa’i, matar gwamnan Kaduna Malam Nasiru Elrufa’i, ta ce mijinta ya faɗa mata cewa ba bu wasu kuɗin fansa da za’a biya idan aka sace ta.
Hadiza ta yi amfani da kafar sada zumunta ta tuwita wajen turo hotunan ta a cikin gonar ta, kamar yadda Legit ta ruwaito

Uwar Gidan El-rufa’i taje duba gonarta, ta ce Mijinta bazai biya kuɗi ba idan aka sace ta Hoto: @hadizel

A jawaban da ta yi, ya yin turo hotunan a kafar sada zumunta, matar gwamnan ta tabbatar da cewa mijin nata ya gargaɗe ta a kan kar taje gonar.
Duk da cewa matar gwamnan bata yi amfani da kalmar ‘Sace mutum’ ko ‘Kuɗin fansa’ ba amma mutum zai iya gane inda maganar ta dosa.
Uwar Gidan El-rufa’i taje duba gonarta, ta ce Mijinta bazai biya kuɗi ba idan aka sace ta Hoto: @hadizel

Bayan ta turo hotunan, Hadiza ta ce:
Gani a gonata, duk wanda ke tunanina to ya daina. Mijina ya riga da ya gargaɗe ni da cewa bazai biya ko sisi ba.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button