Labarai

Sabon Katafaren Gidan Da Ɗan Uwan Buhari Ya Gina A Abuja (Hoto)

Dan majalisar wanda dan uwa ne ga Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci mutane su taya shi murna game da kammala ginin gidan
– A cewar Fatuhu Mohammed, ya dauki kimanin tsawon shekaru hudu kafin kammala ginin dankareran gidan da yace a Gwarimpa Abuja ya gina
Dan uwan Shugaba Muhammadu Buhari kuma dan majalisar wakilai na tarayya, Fatuhu Muhammed ya nuna sabuwar katafaren gidan da ya gina a Abuja, Legit hausa ta ruwaito.
Mr Muhammed, wanda ke wakiltar mazabun Daura/Maiadua/Sandamu a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress APC, ya ce ya gina gidan ne a cikin shekaru hudu.
 

Dan majalisar ya nuna hotunan katafaren gidan alfarmar a shafinsa na dandalin sada zumunta na Facebook inda ya bukaci abokansa da masoya su taya shi da addu’ar nasarar abinda ya cimma.


“Alhamdullilah, na kammala gina gida na a Gwarimpa (Abuja) da ya dauke ni kimanin shekaru hudu ginawa amma don haka dukkan godiya ta tabbata ga Allah kuma ina bukatar addu’o’in ku.
 
“Zan sanar da ranar tarewa a gidan nan gaba,” ya rubuta.
Jim kadan bayan wallafa sakon, dan majalisar ya cire hotuna da rubutun da ya wallafa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button