Nura M Inuwa Yayiwa Masoyansa Magana Mai Ratsa Zuciyarsu Akan Albums Dinsa
Shahararren mawakin nan nura m inuwa yayi magana da kalamai masu hikima wajen masoyansa akan album dinsa.
Ga abinda mawakin yake fadi a shafinsa na sada zumunta.
” @nura_m_inuwa Hakika na sa’ba muku akan rashin sani, na kuma fahimci shiru baza ta gamsar da ku ba, na so ace shirun da nayi yazo da waraka tun kafin ku magantu, sai dai kuma kash bani da iko a hannu, ku kuma ‘kaguwa ta hanaku zuban ido, wannan sai ya dada fahimtar da ni tabbas ba komai zaka so ka samu a lokacin da kake so b, da ni da ku baza mu iya kauda abun da Allah yake son gani ba, amma a karshe ina neman afuwarku ku yafe ni Dan ALLAH. Kamar yadda na fada a baya nayi nawa Allah yayi mini nasa,kuma nasan nan duka mun sani shine dai dai, a karshe ina mai dada baku hakuri, nasan tunda ku kayi hakurin baya mai yawa insha Allah gajeriya gaba ma baza ta gagareku ba, nagode Assalanu alaikum.”
View this post on Instagram
Advertisment
Allah ya taimake Sarkin waka Ya shiga Al’amuran sa mun karbi uzurinka Mahadin waka