Lauwali Danladi matashin da ake zargi ya kashe matar sa akan koko

Rundunar ‘yan sandan jihar Niger ta yi holen wani matashi dan shekara 20 mai suna Lawali Danladi wanda ake zargin ya kashe matar sa sakamakon sabani da ya shiga tsakaninsu da ita, kan kokon da ta dama masa.
Rahotanni sun ce Lawali Danladi ya yin sabanin ya lakada duka ga mai dakin nasa mai suna Zulai Lawal wanda sakamakon haka ta suma kafin daga bisani rai ya yi halinsa bayan an kai ta asibiti.

Danladi Lawal bayan an yi holensa a shalkwatar ‘yan sanda da ke birnin Minna, ya ce, bai taba zaton cewa, duka da ya yi wa matar sa, za ta kai ga mutuwa ba.
‘‘Ban ji dadin yadda ta dama kokon ba, wanda sanadiyar hakan musu ya barke tsakani na da ita, ni kuma cikin fushi shine na lakada ma ta duka’’
‘‘Ban yi zaton cewa, duka da na yi ma ta, za ta kai ta ga mutuwa ba, kawai sabani ne kan dama koko, kuma ban san suma da ta yi, za ta zama ajalinta ba, domin da nasan hakan da ban dake ta ba’’ a cewar Lawali Danladi.
Kamar yadda Freedomradio na ruwaito.Tun farko mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Niger DSP Wasiu Abiodun, ya ce, sun kama Lawali Danladi ne a kauyen Kadaura da ke gundumar Yakila Gunna a yankin karamar hukumar Rafi, bayan sun samu korafi a kansa.

A cewar sa, wanda ake zargin ya amsa laifinsa cewa ya lakada duka wa matar ta sa wanda sanadiyar haka ta suma kafin daga bisani rai ya yi halinsa a babban asibitin garin
Wushishi.Abiodun ya kuma ce, da za ran sun kammala bincike za su gurfanar da wanda ake zargin gaban kotu don girbar abin da ya shuka.