Labarai
Janye Muƙabala: Da alƙalin da lauyan su shirya abin da za su faɗa wa Allah – Martanin Dr. R/Lemo


Advertisment
Malamin nan Dr. Rabi’u Umar Rijiyar Lemo limamin masallacin Jumu’a na Imamul Bukhari da ke rijiyar Zaki ya yi martani kan hukuncin kotu na dakatar da Muƙabala.
A wani saƙo da ya wallafa ta shafin sa na Facebook ya ce, “Da alƙalin da lauyan su shirya abin da za su faɗa wa Allah”.
Bayyana wannan martani da ya yi ya bai wa wasu damar zuwa tare da bayyana ra’ayoyinsu a kai.