Idan kabar Abu dan Allah,Allah zai baka Yaƙi Karɓa Cin hancin Naira Miliyan 1 Anbashi Miliyan Daya Inspector Garba Tabo (Hotuna)




Bayan da rundinar ‘yan sandan jihar Kano ta gano gaskiya, da kuma kokarin da Inspector Garba yayi na kin karban cin hanci don a boye gaskiya, Maigirma Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ya bawa Inspector Garba kyautar kudi Naira Miliyon daya kamar yadda zaku gani a hoto
Wannan hali ne mai kyau kuma abin koyi, duk wanda yayi hakuri ya tsaya ga gaskiya a cikin aikinsa ko rayuwarsa to ba shakka Allah zai kawo masa budi, Inspector Garba yayi hakuri ya guji haram, Allah Ya saka masa da halal akan abinda aka masa tayi na haram ya ki karba
Allah Ka kara wa rayuwar Inspector Garba albarka Amin
Ga hotunan yadda anka bashi kudi nan.










