Kannywood

Hukumar Tace fina finai ta kama mai Waƙen Yabon Annabi Malam Bashir Dandogo

Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta cafke Fitaccen mawakin yabon nan mai suna Malam Bashir Dandago.
Shugaban Hukumar, Isma’il Na-Abba Afakallahu ya tabbatar wa da Freedom Radio faruwar al’amarin.
Afakallahu ya ce, an kama Dandago ne sakamakon wata waka da ya fitar ba bisa ka’ida ba.
A cewar sa, wakar za ta iya tunzura mutane, sannan ya yi gugar zana ga Malaman na Kano kan dambarwar da ke tsakanin su da Malam Abduljabbar Nasiru Kabara.
Sauran wadanda Hukumar ta taba kamawa sun hada da, Sadik Zazzabi, Sunusi Oscar 442, Naziru Sarkin Waka, Muhammadu Buhari (Kosan Waka) da kuma Mu’azzam Idi Yari.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button