Kannywood

Hadiza Gabon Ta Bayyana Babban Abinda Ke Sanya Ta Farin Ciki

Hadiza Gabon, fitacciyar jarumar kannywood ta bayyana babban abinda ke sanya ta farin ciki. Jarumar ta bayyana cewa farantama mabuƙata rai ta hanyar nuna jin ƙai da taimaka musu shine yafi sanya ta farin ciki.
Jaruma Gabon ta bayyana hakan ne a wata hira da tayi da jaridar Dailytrust.

Ta bayyana cewa ta yaya mutum zai ji a ranshi cewa yana da kwanciyar hankali don kawai don shi yana da shi, alhalin akwai mabukata dake kwana basu ci abinci ba.

Yana dakyau mutane su fahimci cewa dan abinda kake ganin ka yi na taimakawa da kyautata rayuwar wasu shine abinda ako da yaushe mutane zasu riƙa tuna ka da shi.”

Hadiza Gabon Ta Bayyana Babban Abinda Ke Sanya Ta Farin Ciki
Hadiza Aliyu Gabon

“Ya na dakyau ako da yaushe mu riƙa ƙoƙarin ganin mun tallafi rayuwar mabuƙatan dake cikin mu.”
A ƙoƙarin ganin ta taimaki mabuƙata, jarumar ta ƙirƙiro wata gidauniya a shekarar 2016. Hadiza Aliyu Gabon (HAG) Foundation, gidauniya ce ta jarumar dake ƙoƙarin tallafa ma mutane musamman ta ɓangaren da ya shafi lafiya. Haka nan ma gidauniyar tana kula da abinda ya shafi ilmi da kuma tallafin kayan abinci.

Jarumar ta kirayi al’umma da su kasance masu nuna so da ƙaunar juna gami da nuna kulawa wanda idan akai hakan za’a rinka samun saukin matsalolin da ake fuskanta a cikin al’umma.
“Za’a rinƙa samun daidaito da cigaba in ya kasance akwai ƙauna gami taimakon juna a tsakankanin al’umma.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button