Labarai

Gwamna Zulum ya yi wa ‘yan gudun hijirar Monguno ruwan nairori A Cikin (Hotuna)

Gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, Babagana Umara Zulum, ya raba N325m da kayan abinci ga magidanta sama da 100,000 wadanda kungiyar Boko Haram ta raba da muhallansu.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna, Isa Gusau, ya fitar ya ce Gwamna Zulum ya dauki matakin raba kudi da kayan abinci ga mutanen ne saboda sun rasa gonaki da harkokin kasuwancinu da saurna harkokin rayuwa sakamakon rikicin Boko Haram.
Kamar yadda Bbchausa na ruwaito.An raba kudu da kayan abincin ne ga mutanen da suke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Monguno, wadanda suka fito daga kananan hukumomin Kukawa, Marte, Ngnazi da Guzamala, a cewar sanarwar.
Ya kara da cewa an raba dubban buhunan kayan abinci da sikari da zannuwa ga magidanta maza 65,000 da kuma mata 35,000.
Ga hotunan nan kasa.
 
 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button