Buhari ya jinjinawa mawaƙa Burna Boy da Wizkid kan lashe grammy
Buhari ya jinjinawa mawaƙa Burna Boy da Wizkid kan lashe grammy
Shugaban Najeriya ya jinjinawa masu salon kiɗan Afrobeats Burna Boy da Wizkid kan samu kyautar Grammys, lambar girmamawa mafi shahara ta 2021.
A wata sanarwa dauke sa hannun mai magana da yawunsa kan harkokin yaɗa labarai, Malam Garba Shehu, Buhari ya ce matasan sun taka muhimmiyar rawa da gudunmawa a fagen wakoki a duniya.
Bbchausa na ruwaito,Sannan ya ce mawaki Burna Boy ya bada muhimmin gudunmawa a fagen wakoki wanda ya kawo wa Najeriya girmama da mutunci a ciki da wajen ƙasar. Ya kuma kara cewa suna alfahari da nasarorinsa.
Hakazalika ya yi jinjina ta musamman ga Wizkid wanda shima ya samu kyautar wakar bidiyon da ta fi ko wacce kyau a wannan shekara.
Shugaban ya kuma ya bi mawaki King Sunny Ade da Femi Kuti wanda hazakarsu ta bada damar shiga wannan takara, da isar da duniya irin salon wakoki da basirar ƴan Najeriya.