Bidiyo : Tirkashi Ganduje yayi Martani Mai zafi akan yimin akan Bidiyon karba Dalla
Amma a lokacin tattaunawarsa da BBC ta awa guda, wani daga cikin al’ummar jihar da suka halarci dakin tattaunawar ya yi tambaya da bukatar ganin gwamnan ya yi bincike kan lamarin, kasancewar yana ƙoƙarin ganin an yaƙi ayyukan rashawa a jihar.
A lokacin da ya yi tambayar, Kabir Dakata na Cibiyar Wayar da Kan Al’umma da Tabbatar da Adalci, KAJA, ya ce “An san mai girma gwamna ya ce zai ƙarfafa gwiwa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa, me zai hana gwamna ya yi duk abin da zai yi domin ganin an bincika maganar zarge-zargen faya-fayen bidiyon Dalar nan domin a tabbatar da adalci a kansu?”
A lokacin da gwamnan ya amsa tambayar ya ce wannan bidiyo da aka fitar ba gaskiya ba ne, kuma ya ce ana bincike a kai kuma za a dauki mataki kan duk wanda ke da hannu.
Ya ce wadanda suka yi bidiyon sun yi ne a matsayin maƙarƙashiya domin hana shi shiga zaɓe, sai dai ba su ci nasara ba.
A ɓangare guda kuma gwamnan ya ce gwamnatinsa ta aiwatar da ayyuka da yawa a jihar, amma kuma a cewarsa har yanzu akwai sauran matsaloli da yawa.
Yana mai shaida cewa gwamnatinsa ta gudanar da ayyuka wadanda za a rinƙa tunawa da shi sama da shekara 100 masu zuwa
Ayyukan da gwamnan ya kafa hujja da su, su ne manyan gadoji da ya gina a birnin Kano, da kuma asibitin Muhammadu Buhari, wanda ya ce an sanya wa kayan kiwon lafiya na zamani.