Labarai

Babu wanda zai rubuta jarrabawar UTME sai mai lambar NIN – JAMB

Hukumar shirya jarrabawar shiga jami’a JAMB ta ce sai dalibi yana da lambar NIN zai iya yin rijistar jarrabawar UTME ta 2021.
Wannan wajibcin ya shafi masu shiga jami’a kai tsaye daga kwalejin kasar ko kuma makarantun gaba da sakandire.
Kamar yadda bbchausa na ruwaito Shugaban hukumar ta JAMB Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja.
“A wannan shekarar za mu yi aiki kafada da kafada da hukumar dake ba da lambaar NIN.
Duk wanda yake son yin rijista da mu sai ya tabbatar yana da Lambar NIN, saboda a wannan shekarar farkon abin da muke bukata ita ce lambar NIN.
Oloyede ya ce duk lambar da aka yi amfani da inda wajen yin rijistar NIN to dole da ita za a ci gaba da amfani ga wanda yake neman gurbin karatu.
Ya kuma ce amma ga daliban da basu da layin waya kuma suna son yin rijista za a iya daga musu kafa.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button