An Bada Belin Bashir Dandago Mai Yabon Annabi Da Hukumar Fina Finai Na kama
Kotun Majistiri mai lamba 58 da ke Noman’sland a garin Kano ta bayar da belin mawakin yabon Annabi mai suna Bashir Dandago.
A yayin zaman kotun na yau Talata, an karanto wa Dandago tuhumar da ake masa wanda ya musanta.
Lauyan sa, mai suna Barista Rabi’u Shu’aibu Abdullahi ya nemi kotu da ta bada belinsa.
Mai Shari’a Aminu Gabari ya amince da bukatar lauyan, inda ya bayar da belin sa bisa wasu sharudda.
Sharuddan sun hada da ya kawo mutane biyar, daya daga ciki ya kasance kwamandan Hisbah na karamar hukumar Gwale,
Har ila yau, daga cikin masu karbar belin ya kasance har da mai Unguwar da mawakin yake zaune, idan ba a samu ba, sai ya musanya da wakilin sa.
Haka zalika kotun ta sanya za a ajiye kudi naira dubu dari biyar.
A jiya ne da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta cafke mawakin, bisa zargin sakin wata sabuwar wakar sa ba tare da Hukumar ta tantance ta ba.
Madogara: Freedom Radio