A shirye nake na fice daga jam’iyar APC matukar masu yi min zagon kasa ba su hankalta ba__Ahmad Bola Tunibu
Ahmad Bola Tunibu ya ce wasu makiyansa da ke cikin gwamnatin APC ne suka hada baki da hukumar ta EFCC don zarginsa da laifin da babu shi kuma bai san shi ba, kawai saboda suna so su bawa siyasarsa matsala don biyan wata bukata ta su ta kansu.
Bola Tunibu ya ce amma wannan ba wani abu bane Wanda zai daga masa hankali, amma tabbas in aka ci gaba da tafiya a haka to zai fice daga jam’iyar ya kafa wata ba tare da wani bata lokaci ba, in ya so duk masu shirin yi masa zagon kasa su cigaba da yi kar su fasa.
Ahmad Bola Tunibu na daya daga cikin jiga-jigan jam’iyar APC, wanda tuni magoya bayansa suka fara tallata shi a Matsayin Dan takarar shugaban Kasa a karkashin inuwar jam’iyar APC a kakar zabe Mai Zuwa ta 2023.
Sai dai kuma masharhanta da dama na ganin wannan tambarin binciken da hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ta EFCC ta fara bugawa a gareshi zai yi mummunan tasiri game da takarar ta shi ta neman shugabancin Najeriya.
Abin jira a gani bai wuce yadda za ta kaya tsakanin hukumar ta EFCC da shi Tunibun ba, Sannan kuma a can gefe guda ga abokan adawarsa na siyasa suma sun zuba na Mujiya.
Daga Kabiru Ado Muhd.