Labarai
Yanzu-Yanzu Farashin Man Fetur Da Ake Baiwa Ƴan Kasuwa Akan Sari Ya Ƙaru Zuwa N180
Farashin man fetur da ake baiwa ƴan kasuwa akan sari ya ƙaru daga N151 akan kowace lita zuwa N180.
Hakan ya faru ne dalilin tashin farashin man a kasuwannin duniya, kuma hakan na alamta cewa farashin man da jama’a ke siye zai ƙaru.
Farashin gangar ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya tashi daga $58 zuwa $63 a jiya. Vanguard ta ruwaito cewa farashin na iya tashi zuwa N190 daga N162 akan kowace lita.
Majiyarmu ta samu wannan labari daga dokin karfe a yayinda kuma Majiyarmu ta samu labarin cewa yanzu haka yan kasuwa mai na Sokoto sun fara rufe gidan mai