YANZU-YANZU: Buhari Ya Nada Dan Shekaru 40 A Matsayin Sabon Shugaban Hukumar EFCC
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattijai da ta tabbatar da Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai, Femi Adesina ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da aka bayar ga manema labarai a yau Talata.
A cikin wasikar zuwa ga Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, Shugaban ya ce yana yin aiki ne bisa ga sakin layi na 2 (3) na Part1, CAP E1 na dokar EFCC ta 2004.
Mista Bawa, mai shekaru 40, kwararren mai bincike ne a hukumar ta EFCC yana da kwarewa sosai a kan bincike da kuma gurfanar da shari’ar Advance Fee Fraud, rashawa ta hukuma, zambar banki, halatta kudaden haram, da sauran laifukan tattalin arziki.
Ya samu horo na musamman a sassa daban-daban na duniya, kuma ya kasance daya daga cikin shugabannin Jami’an EFCC Cadet a 2005.
Mista Bawa ya yi karatun digiri na biyu a fannin Tattalin Arziki, da kuma Digiri na biyu a kan Harkokin Duniya da diflomasiyya
_rariya