Labarai

‘Yan Boko Haram Sun Yi Raga-raga Da Sansanin Sojoji, Bayan Sun Kashe Sojoji Bakwai A Jihar Barno

Daga Comr Abba Sani Pantami
Akalla sojojin Nijeriya bakwai ne su ka mutu bayan wani harin bazata da kungiyar Boko Haram su ka kai wa wani sansanin sojoji.
Sojojin da abin ya shafa sun fito ne daga Bataliyar 153 da ke Marte, a Jihar Barno
Wata majiya daga cikin sojoji ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa Boko Haram din sun shammaci sojojin ne wajen karfe 10 na safiyar ranar Litinin.
Amma daga baya sun yi karfin halin da su ka kare sansanin, kuma su ka kori Boko Haram din.
Majiya ta ce an shammaci sojojin ne, kuma karfin makaman da Boko Haram din su ka je da su, ya girgiza sojojin matuka.
Bayan ragargaza sansanin sojojin ne kuma sai aka kwashe sojojin da su ka rage daga Marte din aka nausa da su wata karamar hukuma.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button