Uncategorized

Yadda Bilyaminu ya caka wa Shafa’atu wuka a kotu bayan alkali ya raba auren su

Wani magidanci mai suna Bilyaminu Abdullahi ya caka wa matarsa Shafa’atu Sule wuka da wani dan uwan ta a kotu bayan alkali ya raba auren sa da Shafa’atu.
Shafa’atu ta kai karar Bilyaminu kotu don a raba auren su. Bayan sauraren hujjojin su duka, alkalin kotu ya amince da bukatun Shafa’atu sai ko ya yanke hukuncin su rabu.
Kamar PREMIUM TIMES na ruwaito.Sannan kuma ya umarci Shafa’atu ta maida wa Bilyaminu kudin sadakin ta da ya biya.
Wannan hukunci bai kwanta wa Bilyaminu a rai nan take sai ya fallo sharbebiyar wuka a gaban alkali ya ko daba wa Shafa’atu sannan ya juya kan dan uwanta da ya rako ta kotu shima ya sharba masa wukar.
Nan take ‘yan sanda suka cafke Bilyaminu.
Kakakin ‘yan sandan Kano Abdullahi Kiyawa, ya bayyana cewa Bilyaminu ya yi danasanin aikata abin da yayi a Kotu.
” Biyaminu ya shaida wa ‘tan sanda cewa yayi iya kokarin sa na ganin bai rabu da matarsa Shafa’atu ba, Amma wanta Sule ya ki yarda. Yace ya tura magabata su je su ba su hakuri kada a raba auren amma sam sun ki yarda.
Ya ce yana son matarsa kuma bai yi zaton abin zai kai ga har a warware auren ba.
Sai dai kuma tun a farko Shafa’atu da ‘yan uwanta suce rashin kula da gallaza mata azaba da bilyaminu yake yi ne ya kaita da ‘yan uwanta makura.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button