Addini

Wayar Dr. Rabi’u R/lemu Da Shugaban Kogo Abduljabar Akan Su Hadu Domin Su Tattauna



Via:- Garkuwan Magabata
NA KOGO:Yanda ka rubuta a takardar sunan maudu’ai ne kawai,kamar yanda ka rubuta cewa kore abubuwan da akwai sai ka rubuto mani su.
R/LEMU: A’a malam duk duniya ba inda ake tattauna haka, idan za’a tattauna topic kawai ake bayarwa ya rage ga abokin tattauna yaje yayi nashi bincike.
NA KOGO: ka rubuto mani hujjojinka sai nayi tahaqiqi sai in kira ka mu zauna.
R/LEMU:daga baya kenan, ai ba inda ake yin munazara a haka duk duniya ka ce wai sai abokin tattaunawarka ya fada maka hujjojinsa sannan daga baya ka kira sa ku zauna. Kuma duk abinda ka rubuta a cikin muqaddima sai da ka kare bincike sannan ka rubuta shi.
NA KOGO:A’a ban kare ba
R/LEMU: To malam daga nukudodin nan guda biyar ko wane zan rubuto maka misalai guda uku-uku
NA KOGO:Eh ban jinka wayar na rawa, to amma wayar na rawa
R/LEMU:Amma ba akan su ba kawai zamu zauna ba. Ka shiga youtube kaga yanda ake munazara kala-kala.
NA KOGO:A’a ni bana karatu a youtube a littafai nake karatu.
R/LEMU:Akaramakalahu ai ba karatu ake a youtube ba hotuna masu motsi ake gani
NA KOGO:don Allah malam rabi’u so nake mu tattauna a matsayin masoyan juna amma ba magauta ba, ka ce ina gaida Doctor.
R/LEMU:To ai kai ka ke cewa idan kana karatu duk mai abin fada yazo, to ka kaddara kana cewa haka a cikin kogo sai nazo cewa zaka yi sai ka bincika. Sai idan malam tsoro yake a tattauna akan muqaddima, kuma kai kake neman a zauna fa?
NA KOGO:eh tsoro nake ji. Malam rabi’u ka bani mamaki.
R/LEMU:A’a malam kai ka bani mamaki domin kai kake cewa ko kwana kake dan salafiyya yazo sai ka kure shi. Ashe ba zaka iya ba.
R/LEMU:Amma Akaramakallah daga yau idan kana karatunka ka daina cewa idan da mai abin fada yazo tun da ko mai abin fadar yazo ba zaka saurare shi ba.
NA KOGO: To na daina!
NA KOGO:Malam rabi’u yanda kuke fassara ni ba haka nake ba.
R/LEMU: Ai maganganun mutum suke fassara ko waye shi.
NA KOGO: Mu tattauna akan matsalar tauhidi, a littafenka ihya’u aqida da Alkashif. Domin ba matsala bace da zan yi rubutu akanta ba a kirji take. Matsalar muqaddima za’a jawo mazajen hadisi ne kaga ni ba mahardaci bane
R/LEMU:Ni bani tsoro mu tattauna akan komai. Amma kamar yanda kake fada cewa littafen muqadima ya hanamu bacci shine nake so mu tattauna aka muqadima ta 1&2
R/LEMU:Me yasa kake tsoron a tattauna akan muqadima?
NA KOGO:A’a ba tsoro nake ji ba amma ka rubuto mani hujjojinka
Lalle hausawa sun yi gaskiya da suke cewa”Allah wadaran naka ya lalace” ni dai da na rike irin wannan ruku6ub a matsayin malami wallahi kara babu da shi. Iyakarsa hafshi da hargowa a gaban yan kogo kuma cikin kogo . Ba su tsayawa a tattauna akan maudu’i gudu sai su yi ta tsallake-tsallake idan suka dauko rigimar da basu iyawa sai su koma wani wurin misali sun dauko rikicin akan sayidina mu’awiya r.a sun kasa, sun komacaque wajen qaribullah sun kasa, yanzu sun koma wajen yan inyas. Na tabbata duk mai cewa azo a zauna jahili ne, zama da yan kogo 6ata lokaci ne domin su suna kawai suke nema ba gaskiya ba. Ko wane jahili ya fito a kogo da warin bakinsa wai ayi muqabala da shi. Yanzu shi na kogo ya yadda da mukaddima amma kuma ba zai iya kare abinda ya rubuta ba to ina ga dan shan miyar kogo? dan abi shata asha kida?
Wai a fada masa hujjoji yaje yayi dubaru.Abin mamaki baya karewa wai mutum ya rubuta littafe da kansa amma bai iya kare shi anya ko gaskiya ce aka rubuta a ciki? Matsoracin kare mai hafshi daga nesa……….. Allah ka karya karya makaryata da masu tallar karya.
Ga mai sha’awar saurare da sautin nan









Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button