Uncategorized

Wasu Mahiman Wurare Guda 6 A Jikin Mata Da Suka Fi Dauke Hankali Maza

Duk namiji da irin abunda yake son ganin mace dashi a halitta. Ba kamar yadda wasu suke dauka ba. Wasu mazan ba kyau fuskar mace ko launinta ke daukar musu hankali ba. Wasu muryar mace kadai ya wadatar dasu su ji sun kamu da soyayarta.
Sai dai kuma akwai wasu mahmman wuraren da aka yi ittifakin sune suka fi daukar hankali maza. Wanda yana da wuya mace mai wadannan abubuwan a halitta ta kasa ganin Maza masu sha’awar wannan baiwan nata suna mata ribibin su mallakeshi ta hanyar aurenta ko kuma su ribace ta ta hanyar yaudaranta.
1: Karamin Baki: Mace mai karamin baki tana dauke hankali maza. Domin kashi 60 maza a cikin 100 basu cika sha’awar mace mai girman baki ba.
2 : Idanu: Maza suna son ganin mace mai kyau halitta na idanu. Irin idanuwan nan da ake musu lakabi da golden eyes. Idanuwa ne bincike ya tabbatar da maza da dama suna samun shauki da zaran sun hada Idanuwa da mace mai wannan baiwar.
3: Gashi: Mace mai gashi bama ga maza kadai ba. Hatta yan uwanta mata suna sha’awar ta. Don haka yasa a cikin jerin ababain da maza suke tabbatar da kyauace gashin kanta na ciki. Duk kuwa da akwai mazan da suke son mace mai gashi a jikin ta ko giran idanuwan ta.
4: Nonuwa: Kowoni namiji yanada siffar irin nonuwan da suke dauke masa sha’awa da kuma jawo hankalinsa wajen mace. Wasu mazan mata masu manyan nonuwa suke so, wasu kuwa madaidaita, akwai kuma mazan da sun fi sha’awar ganin kirjin mace mai nonuwa irin na kirgen dangi, wannan ke sa suji suna son mace.
Koma wani irin siffa namiji yake son ganin nonuwan mace dasu. Babu tantama nonuwan mace na cikin jerin manyan halittun ta da ke dauke wa namiji hankali. A duk irin yanayin halittan nonuwan ta, akwai maza masu tarin yawa da irin sa suke sha’awa.
5 : Duwawu : Suma dai tamkar Nonuwa suke. Domin ko wani irin namiji da irin duwaiwukan da suke jawo hankalinsa.
Akwai masu son ganin duwaiwa masu tudu. Akwai masu son ganin mace da madaidaicin duwawu, akwai mazan suna ganin mace wacce shamalo babu komai a bayan ta.
6: Tsawo: Babu shakka fiye da kashi 70 na maza suna son ganin mace doguwa. Sai dai wannan ba yana nufin cewa mata marasa tsayi basu dauke hankali maza bane, sai dai mata masu tsayi sun fisu kasuwa.
Wannan nazarin ba wai yana nufi su kadai ne halittu mata da suke dauke Hankalin maza ba. Kuma macen da bata da irin wannan halittan da aka ambata ba ana nufin maza ba zasu so ta bane. Su maza shu’umai ne, abunda wani baya so a jikin mace, shi wani yake nema ruwa a jallo.
#tsangayarnalam

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

2 Comments

  1. Irin wadannan bayanai suna kara ilmantar da mutane da dama wasu muhimman al’amurra da ya kamata su sani amma suka jahilceshi.
    Sai dai yana da kyau ku ringa kyautata irin kalmomin da kuke amfani da su, domin dalilan tsaro ba don tsoro ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button