Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ke Najeriya Sheikh Ahmad Gumi ya ce ba shi ne ya zargi sojojin kasar cewa ba sa son kawo karshen matsalar tsaron kasar ba saboda suna samun wani abu game da rashin tsaron da arewacin kasar ke fama da shi.
Malamin ya shaida wa BBC a hirar da muka yi da shi ta manhajar Zoom cewa makiyayan da ya tattauna da su sun gaya masa cewa sojoji ba sa son matsalar tsaro ta kare a arewacin Najeriya.
“A’a ba na ce wai ba sa so ba ne… su kansu mutanen makiyayan su ne suka ce ai mutanen tsaro ba sa son wannan abin ya kare domin kudin da suke yi, kuma hakikani mun yi kokarin haduwa da masu tsaro, mun lura ‘yan sanda suna ba mu hadin kai amma ba ma samun hadin kai daga soja domin haduwa ma da shugabannin nasu wani aiki ne,” in ji malamin.
Ya jaddada kiran da ya yi cewa yin sulhu da ‘yan fashin daji shi ne mafita daga hare-haren da ake kai wa yankin arewacin kasar, yana mai cewa kodayake wasu gwamnoni na ganin hakan ba shi da alfanu amma wasu suna cin moriyar hakan.
A cewarsa: “Akwai gwamnonin da kuma suke ganin sulhun shi ne hanya kuma sun yi sulhun an samu sauki. Idan ka je Zamfara, da tsakanin Gusau zuwa Shinkafi kamar hanyar Birnin Gwari ne. Amma yanzu idan ka je ga shi nan mutane suna kiwonsu suna noma. Ashe ka ga kenan sulhu yana amfani.”
Ga bidiyon nan ku saurara.
Sheikh Gumi ya ce sojojin Najeriya ba sa ba shi hadin kai a kokarin yin sulhu da yake yi da barayin daji. Malamin ya ce bayan shiga daji yin sulhu da ya yi a Zamfara, tubabbun barayin sun ce sojoji sun je wurin sun jefa masu bam. pic.twitter.com/ZkR071jyrD
— BBC News Hausa (@bbchausa) February 12, 2021