Labarai
Saudiyya ta rufe Masallatai saboda saɓa ka’idojin korona
Gwamnatin Saudiyya ta rufe wasu masallatai bayan an samu cikin masu ibada da suka kamu da cutar korona.
kamar yadda bbchausa na ruwaita Ma’aikatar lamurran addini ta ƙasar ta ce masallatai biyar ne aka rufe, huɗu a Riyadh babban birnin ƙasar da kuma ɗaya da ke kusa da kan iyaka a yankin arewaci, kamar yadda kamfanin dillacin labaran ƙasar ya ruwaito.
Masallatai kimanin 57 yanzu Saudiyya ta rufe cikin mako ɗaya, yayin da aka buɗe 44 daga cikinsu bayan an yi masu feshi da kuma gindaya sharaɗi ga masallata.
Gwamnatin ta buƙaci mutane su kiyaye sharuɗɗan korona tare da bayar da rahotanni kan duk masallacin da ya saɓa dokokin.