Labarai

Satan Dalibai A Kankara Jahar Katsina Ana Zargin Kantoman Jibiya dasa hannu (Hoto)

Advertisment

‘Yan Sanda Sun Cafke Tsohan Kantoman Karamar Hukumar Jibia Bisa Zargin Taimakawa ‘Yan Bindiga A Jihar Katsina
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ta kama tsohan Kantoman Karamar Hukumar Jibia, Alhaji Haruna Musa Mota bisa zargin taimakawa tare da hadin bakin da kuma ta’addancin yan bindiga a jihar Katsina.
Kakakin rundunar SP Gambo Isa ya tabbatar wa Blueink News Hausa ta waya cewa tabbas mun kama shi bisa zargin taimakawa tare hadin baki da yan bindiga, da suka addabi wasu kananan hukumomi. Kuma tuni aka maka shi gaban kuliya domin yi masa Sharia. Tun daga wayar da ya yi da su yan bindiga, muka fara bincike, cewar kakakin.
 
 
 

Asalin hoto da rahoto daga Alfijir Hausa page

Kama shi bai rasa nasaba da wata waya da aka nada inda aka jiyo shi yana waya da wani jagoran ‘yan bindiga, suna tattaunawa dangane da kudin da yake cewa gwamnati ta cire da abinda aka ba su.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

  1. Wannan irinsu gurbata kasane, yakamata abincikeshi da kyau har sai ya tonama abokanan harkar asiri. Sanan asan wane mataki za a dauka akansu. Amma nidai ganina in hartatabata gaskiya to kashesu shine adalci ga kasarmu mai albarka. Sunsa muna zargin shugabaninmu akan kisan gilla da a kemana a kasarmu mai albarka. Wannan itace shawarata amadadin al umar gobir daga s.s.gobir

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button