Pantami ya ƙara wa’adin haɗa lambar NIN da layukan waya
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta tsawaita wa’adin haɗa lambar ɗan ƙasa ta NIN da layukan salula wanda ake gudanarwa yanzu haka da kusan wata biyu.
Ministan Sadarwa Dr. Isa Ali Pantami ne ya bayyana hakan yayin wani taron ministoci kan haɗa lambar NIN da lambar waya a jiya Litinin.
Yadda Bbchausa na ruwaito.Rahoton ƙarin wa’adin na cikin wata sanarwa ce da shugaban sashen sadarwa na hukumar samar da katin ɗan ƙasa ta NIMC ya fitar a yau Talata, inda Pantami ya ce za a ci gaba da aikin har zuwa 6 ga watan Afrilun 2021.
Ya ce an ɗauki matakin ne domin bai wa ‘yan Najeriya da kuma ‘yan ƙasashen waje damar haɗa lambobin nasu da layukan wayarsu.
Sanarwar ta ce ya zuwa yanzu kamfanonin sadarwa sun karɓi lambar NIN ta mutum miliyan 56.18.
“A mataki na tsakatsaki, kowace lambar NIN na ƙunshe da lambobin waya uku zuwa huɗu, kuma hakan na nufin wannan adadi shi ne na mafi yawan layukan wayar da ke aiki a yanzu,” in ji sanarwar.