Labarai

Najeriya za ta taimaka wa Mozambique wajen yaƙi da ta’addanci

Advertisment

Najeriya ta yi tayin taimaka wa ƙasar Mozambique a yaƙin da take yi da ta’addanci a yankin Cabo Delgado mai arziƙin iskar gas.
Fiye da mutum 2,000 aka kashe sannan aka raba wasu fiye da 500,000 da muhallansu a rikicin, a cewar hukumar ICRC.
kamar yadda bbchausa na ruwaito.Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya ziyarci Mozambique a ƙarshen makon da ya gabata, inda ya gana da Firaminista Carlos Agostinho do Rosário.
Mista Onyeama ya ce Najeriya ta shirya taimaka wa Mozambique da ƙwarewarta ta yaƙi da masu da’awar kishin Islama.
Ziyarar wani ɓangare ne na ziyarar diflomasiyya zuwa ƙasashen kudancin Afirka don nemar wa Najeriya goyon baya a ƙoƙarinta na samun shugabancin kwamitin tsaro na Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU).
Tanzaniya da Afirka Ta Kudu da kuma Burkina Faso ma na neman kujerar.
Za a yi zaɓen ne a mako mai zuwa a wajen taron ƙungiyar ta AU.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button