Mawaki Nura M Inuwa Yayi Martani Da Kalamai Masu Hikima Akan Kama Darakta Mu’azzam Idi Yari
Gamar wasu jaruman Kannywood suna da martani game da kama dan uwar sana’arsu babban darakta Mu’azzam Idi Yari wanda yanzu haka yana gidan yari ta Gidan sarki a jahar kano wanda duk wanda yayi martani a cikin jaruman Kannywood zamu kawo muku labarinsa.
Shi nura M inuwa yayi kalamai masu hikima akan irin yadda wannan darakta ya bashi gudumuwa sosai a masana’antar wanda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ga abinda yake cewa.
“Shi yayana ne kuma ya bani gudunmawa fiye da kowa a wannan masana antar, shine yayi tallana a lokacin da wasu ke ganin kamar yana tallan turmi ne, duk lokacin dana shiga damuwa ya kanji kamar shine a cikinta, a wannan lokacin da yake cikin wannan hali nima inaji kamar nine a cikin halin da yake ciki, ina fatan wannan jarraba ta zame maka alkairi a gaba, Allah ya zama gatan ka alfarmar Annabi sallahu alaihi wassalam.”