Labarai

Kotu ta kori ƙarar matar da ake zargi ta kashe mai aikinta a Kano

Wata kotun majistare da ke Kano ta sallami ƙarar matarda ake zargi ta Kashe mai aikinta a kwanakin baya.
Zaman kotun da ke Gyadi-gyadi a Kano, Mai shari’a Ibrahim Khalil ya ce an sallami wadda ake karar ne saboda roƙon da lauyan gwamnati ya yi na a sallame ta saboda rashin ƙwararan hujjojin da za su tabbatar da laifin da ake tuhumarta da aikatawa.
Kamar yadda BBCHAUSA na ruwaito, Lauyan gwamnatin ya gabatar wa da kotu kwafin shawarar ma’aikatar shari’a kan ƙarar da ke nuna a soke tuhumar a kuma sallame matar saboda rashin hujjojin tuhuma.
 
 
 
 

Wannan shine hoton da anka fitar bayan korafe korafe fuskar tar da ake zargi

Sannan ta buƙaci a yi bincike kan ƴan jaridar da suka yayata batun tun gabanin kammala bincike da wasu mata biyu da ake zargin bayar da bayanai ga ƴan jaridu da ba na gaskiya ba. Wanda idan an same su da laifi za a gurfanar dasu a gaban kotu.
Yanzu kotun ta kawo ƙarshen tuhumar da ake yi wa matar kuma ta sallame ta.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button