Kadan Daga Aika-aikar Abduljabbar kabara Goma Sha Hudu Ga Sahabbai Da Manzon S.a.w
Daga Ustaz Aliyu Imam Indabawa
Abduljabbar Nasiru Kabara:
1. Ya ce Nana Aisha ba ta yi imani da mijinta Annabi ba ne kwata-kwata.
2.Ya ce sayyaduna Usman Dan jari hujja ne a lokacinsa masu kudi suka kara kudi talakawa suka kara talauci a bisa haka ne sahabbai suka taru suka kashe shi.
3.Ya ce Abdullahi dan Umar munafiki ne mai karbar cin hanci da rashawa.
4.Ya ce Abu hurayra tataccen makaryaci ne da ya kitsa hadisan karya ga annabi kuma a yau suka cika littafai.
5. Ya ce Anas makaryaci ne munafuki.
6. Ya ce sahabiya ummu sulaym Mahaifiyar Anas R’A mahaukaciya ce tana da tabin hankali kuma ita ce Fulana da aka ambata a wani hadisi.
7. Wanda ya ce Annabi S.A.W ya dauki dan zina a matsayin sakatarensa yana rubuta masa wahayi kuma bai yi imani da Annabin ba har ya mutu.
8. Wanda ya ce munafukai ne suka kewaye Annabi kuma sune suka hana ya rubuta yadda yake so su rayu bayansa kuma su kai munafurcin rusa wasicinsa na ranar Ghadir.
9. Wanda ya ce Nana Aisha da Hafsa suna ta kulle kulle sanda Annabi S.A.W yana rashin lafiya kafin watafinsa.
10. Wanda ya ce Alqur’anin da ke wajenmu ba ingantacce ba ne.
11. Wanda ya ce Annabi bai je sama mi’iraji ba. Kuma alqur’ani ma ya tabbatar da Mi’iraji.
12. Wanda ya ce babu tambayar kabari da tashi daga cikinsa.
13. Wanda ya ce babu mutanen da ke karyata junansu kamar sahabban Annabi S.A.W
14. Wanda ya qundumawa Annabi muhammad S.A.W zagi ya ce a whatsapp aka turo masa yana da audio, amma har yau bai fitar da audion ba
Wannan bai kai kashi biyar cikin dari na aika-aikarsa ba. Allah ka shaida na tsani Abduljabbar Kabara tare da duk mai goya masa baya kamar yadda ya tsani Annabi da matansa da sahabbansa da bayin Allah nagari.
Allah Ya jaddada la’ana a gare shi.