Labarai

Idan Sun Gama Da Fulani Kan hausawa zasu dawo Irin Yadda anka lalata kayan Hausawa A Jahar Oyo (Hotuna)

Lokacin da muke ta kokarin fahimtar da al’umma cewa tsangama da kyamar da ake nunawa fulani a yankin kudancin Nigeria ba’a ana yi don kasancewarsu fulani bane, ana yi ne don sun kasance daga yankin Arewa ne, amma mutanen mu basu gane ba, har akwai masu cewa ba laifi bane don mutanen kudu sun kori fulani, saboda fulani sun zama annoba
Kiyasa ya nuna sama da fulani dubu 5 ne suka bar yankin kudu saboda gujewa harin ta’addanci da ake kaddamar musu a kullun, yanzu sun kokari fulani sun dawo kan Hausawa, ga nan ta’adin da Sunday Igboho da jama’arsa suka yiwa Hausawa a garin Ibadan jihar Oyo, wannan shine target din su, wato su kori mutanen Arewa ba wai fulani kadai ba
Datti Assalafy ne na wallafa.A garin Ibadan, bayan duk wannan ta’addanci da aka yiwa Hausawa, abin ya kai ga sai sun biya jami’an tsaro kudi daga Naira dubu 20 zuwa sama kafin su yi rakiyar Bahaushe zuwa gurin da zai samu mafaka daga harin ta’addanci
Shiyasa muke cewa kar mu yadda mu Hausawa ko ince mu mutanen Arewa a jefa tunanin kabilanci tsakaninmu da ‘yan uwa Fulani, duk abinda yake faruwa tsarawa akayi, kuma karshe abinda ake so shine a tayar da yakin kabilanci a Nigeria, tunda sun gwada hanyoyin tayar da yaki ba su ci nasara ba
Yanzu da ace mutanen Arewa zasu kufula su afkawa mutanen kudancin Nigeria da suke da zama anan Arewa to da shikenan kasar ta fada cikin rikici da zaiyi sanadin ruguzata, kuma wannan ake so ya faru
Don haka muke amfani da wannan damar don fahimtar da jama’ar mu cewa bai kamata mu dauki fansa akan ‘yan kudu da suke nan Arewa ba, addinin mu na Musulunci ya haramta mana daukar fansa akan wanda bai taba mu ba
Muna rokon Allah Ya zaunar mana da Nigeria lafiya, Allah Ya kunyata wadanda suke adawa da zaman lafiyar mu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button