Fadawan Shugaban Kasa Sunyi Shiru Ana Kisan ‘Yan Arewa A Jihar Oyo
Daga Ustaz Engr. Ibrahiym A. El-Caleel (Daya daga cikin Daliban marigayi Malam Albaniy Zaria) yace:
Yanzun nan na duba shafin Twitter da Facebook na shugaban kasa Buhari da shafikan masu tallafa masa da yada labarai Garba Shehu, Femi Adesina da Bashir Ahmad
Amma babu sanarwa a hukumance daga garesu akan kisan kare dangi da ake yiwa ‘yan Arewa a jihar Oyo, magana ta gaskiya, shi kam Bashir Ahmad ma sako ya fitar ta shafinsa na Twitter akan wasan kwallo awanni 20 da suka gabata
Wannan shine shugabanci mai kyau ko? jinjina gareku
Engr Ibrahiym yaci gaba da cewa:
Daga zamanin mulkin Obasanjo zuwa kan Goodluck Jonathan munga yadda suke kokarin daukar matakin gaggawa na sanya dokar ta baci a jihohin da Gwamnoninsu suka kasa daukar mataki akan matsala na tsaro, ko ba komai sunyi kokari ko da gaggawar daukar matakin baiyi aiki ba
Amma a wannan Gwamnatin ta al’umma mai tarin jama’a masoya, gwamnatin da aka nuna mata tsananin soyayya a tarihi, amma abinda kawai jama’a zasu samu shine shiru..
Shirun da wannan Gwamnatin take yi ana cutar da wasu jama’a ya faro ne tun daga farkon wa’adin mulkin shugaba Buhari, amma a haka aka sake saka masa da wa’adin mulki karo na biyu, abinda mutane suka zaba ne, don haka sai su karba
Wannan babban darasi ne ga ‘yan Nigeria da ya kamata su koya, shugabanni na kwarai ba wai dole sai idan sun fito faga kabilarku ko karamar hukumar garinku ba, abinda kawai ake bukata shine shugabanni na kwarai, shugaban da kuke son sa yana son ku, ba wai shugaban da kuke so shi baya son ku ba. ~ Engr Ibrahiym A. El-Caleel
Majiyarmu ta samu daga shafin Hausaloaded
Allah Ka bamu mafita na alheri