Dr Ahmad Gumi A Zamfara: Amsa Gayyatar Gwamna Tare Da Kira Zuwa Ga Al’ummar Fulani Don Su Zauna Lafiya Da Juna
A jiya ne Majiyarmu ta samu wannan labari a shafin babban malamin akan irin wannan aiki da ya dauko wanda tabbas rashin ilimi ne ke sanya Fulani irin wannan aika aika wanda jiya ya shiga jahar mahaifinsa wato Sheikh Abubakar Mahmud Gummi Allah ya jikansa da rahama.
Ga jadda sunka wallafa jawabin gayyata.
“Wannan tafiya da Sheikh Dr. Ahmad Gumi yayi domin amsa kira tare da gayyata da gwamnan Jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle (Matawallen Maradun) domin tattaunawa da Malam tare da nuna mishi wadansu aikace-aikacen da yayi domin tsugunar da Makiyaya a wuri guda.
Bayan saukar Malam ke da wuce tare da gabatar da Sallar Azahar da La’asar Kasaru, ba tare da bata lokaci ba Malam ya wuce Karamar Hukumar Maradun inda Malam ya shiga dajin Makiyayar Sarkida domin ganewa kansa aikin Biliyoyin Nairori da Gwamnan Jihar Zamfara yayi domin samarwa da Fulanin Jihar Zamfara wurin da zasu rika kiwo.
Wuri ne da Gwamnan Jihar Zamfara ya gina domin kawo karshen yawace-yawacen da al’ummar Filani take yi inda ya sama musu wurin da fadinsa ya kai eka 2280 inda aka gina musu gidajen kwana sama da 250 tare da gina madatsun ruwa domin shayar da su da dabbobinsu da gina makarantun Islamiyya da Boko har zuwa Sakandare da gina babban asibin mutane da dabbobi da samar musu da Masallacin Juma’a da wuraren wasanni da motsa jiki.
Tafiyar wacce ta samun rakiyar Babban Limamin Masallacin Sultan Bello Sheikh Dr. Muhammad Sulaiman Adam da Farfesa Usman Yusuf tsohon shugaban NHIS na kasa baki daya tare da tsohon Dan Majalisar Tarayya – Hon Rufa’i Ahmad Chanchangi da Alhaji Buba tsohon Dan Majalisar Jihar Bauchi tare da Malam Tukur Mamu shugaban Jaridar Desert Herald da manyan Malamai da Alarammomi da Dalibai baki daya.
Manyan jami’an gwamnatin Zamfara suka tarbi Malam tun kafin shigowarsa garin Gusau.
In dai baku manta ba, tun a farkon watan Janairun 2021 Malam ya fara shiga dazukan jihar Kaduna domin tattaunawa tare da al’ummar Filani domin samun dawwamammen zaman lafiya. Mafi yawan garuruwan da Malam ya ke shiga yana daura tubalin ginin Makaranta da Masallacin da Asibiti da wurin sa’a wanda hakan shine kawai hanyar da za a iya yanke dukkan wata jijiya da ta kafu ta mayar da al’ummar Fulani ‘yan ta’adda tare da kusanto dasu cikin al’umma baki daya.”
Salisu Hassan Webmaster
08038892030
01/02/2020