Dakan ɗaka…: Ɗiyar Rikadawa ta auri yaron baban ta
ALHAMDU lillah, yau dai alƙawari ya cika. Tun kusan makonni biyu kenan da aka yaɗa katin gayyatar ɗaurin auren ɗiyar fitaccen jarumi Rabi’u Rikadawa da jarumi Salisu Abdullahi (Babangida) a soshiyal midiya.
A yau Juma’a, 5 ga Fabrairu, 2021 aka ɗaura auren jarumin da santaleliyar sahibar tasa Fatima Rabi’u Rikadawa.
An ɗaura auren da misalin ƙarfe 1:20 na rana, bayan sallar Juma’a a masallacin Kabala Junction da ke Titin Nnamdi Azikiwe (Bypass) a kan sadaki N100,000.
‘Yan fim da mawaƙa daga Kano da Kaduna da dama sun halarci ɗaurin auren. Wasu daga cikin su sun haɗa da Malam Musa Abdullahi, Sani Musa Danja, Adam A. Zango, Al-Amin Ciroma, A.S. Muhammad, Malam Aminu Saira, Kamal S. Alƙali, Alhassan Kwalle, Abubakar Yarima, Nasiru Ali Ƙoƙi, Wassh Waziri Hong, Jamilu Adamu Kocila, Kb 2-Effects, Nura M.C, El-Mu’az Birniwa, Balarabe Jaji, Nasiru Gwangwazo, Ɗayyabu Olatunji, da sauran su.
Bayan ɗaurin auren an shirya ƙasaitacciyar walima a wani gida kusa da masallacin da aka ɗaura auren.
An yi walimar a wani ɗakin taro, inda a nan aka ci aka sha. Babu wani wanda ya halarci walimar da zai ce bai ci abinci ba. In ma ba za ka ci a wurin ba, za a ba ka ka tafi da shi. Kuma abin sai wanda ka zaɓa, domin har da abincin Yarbawa a wurin, wato amala.
Mahaifin amarya kuwa duk wanda ya gani zai tambaye shin ka samu abinci kuwa? In sau goma ku ka haɗu sai ya yi tambayar.
Biki ya yi biki, kowa sai yabawa ya ke yi.
Wannan walima ba ga ‘yan fim da sauran waɗanda aka gayyata ba kawai, har da ‘yan unguwar yau sun ci sun sha.
Wannan aure dai ‘yar gida ce aka yi, wato abin da ake ce wa dakan ɗaka shiƙar ɗaka, domin kuwa duk wanda ya san Rabi’u Rikadawa, to ya san shi da Babangida, don wasu da dama Babangida Rikadawa su ke kiran sa da shi.
Wasu kuma sun ɗauka ɗan sa ne, yayin da wasu kuma ke ganin ɗan’uwan sa ne.
Babangida dai yaron Rikadawa ne na industiri. Kuma ga shi yanzu an ƙara ƙarfafa danƙon zumunci, ya kuma zama ɗaya daga cikin ‘ya’yan Rabi’u Rikadawa yanzu.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.
Allah yabada zaman lafiya muma in namu yazo allah yabamu mata masu addini amen
Amen