Labarai
Da Duminsa:APC na shirin tsayar da Goodluck Jonathan da El-Rufai takara a 2023
Wani rahoto ya bayyana cewa jam’iyyar APC na shirin tsayar da Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan da Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a matsayin ‘yan takara a zaben shekarar 2023
Wata majiya ta bayyanawa Sahara Reporters cewa za’a tsayar da mutanen 2 ne saboda kowane daga bangaren da ya fito yana da mabiya kuma ana sonsa.
Akwai dai matsin lamba akan tsohon shugaban kasan da ya koma jam’iyyar APC, kamar yanda Rahoton ya nunar.
Hutudole na ruwaito.A baya dai, Tawagar ‘yan APC din daya hada da gwanoni sun kaiwa Goodluck Jonathan ziyara amma daga baya suka musanta cewa ba nemanshi ya tsaya takara suka je yi ba.