Caccakar Buhari: DSS ta cafke hadimin Ganduje, Dawisu, bayan yace APC ta gaza


Hukumar tsaro ta fararen kaya (DSS) ta damke Salihu Tanko-Yakasai, mai magana da yawun gwamna Kano, Abdullahi Umar ganduje bayan ya ce gwamnatin APC ta gaza.
A ranar Juma’a, Tanko-Yakasai ya bayyana damuwarsa a kan labarin kwashe yara mata na makarantar sakandaren kwana da ke Jangebe a jihar Zamfara
Bayan sa’o’i kadan da yin tsokacin a shafinsa a Twitter, an nemi Yakasai ko kasa ko sama an rasa, Legit ta wallafa.
Amma a wata wallafa da shafin Twitter na jihar Kano yayi, an sanar da cewa Tanko-Yakasai na tare da jami’an tsaron farin kaya.
A wallafar da Yakasai wanda aka fi sani da Dawisu yayi a shafinsa na Twitter bayan samun labarin satar ‘yan matan daga makarantar Jangebe, ya bukaci gwamnatin APC da ta kawo karshen ‘yan ta’adda ko tayi murabus.