Kannywood

Babbar Magana:Da a gina masallatai da islamiyyu gwanda a zuba kudin a harkar film ~ Aminu Momo

Aminu Abdullahi
Fitaccen jarimin masana’antar Kanywood Aminu Saharif Momo ya ce Ya ce a yanayin da ake ciki yanzu da a gina masallatai da islamiyyu gwara a zuba kudaden a harkar shirya fina-finan hausa.
Kano Focus ta ruwaito Momo ya bayyana hakan ne cikin shirn ‘Barka da hantsi’ na gidan rediyo freedom da safiyar yau Laraba.
Ya ce zuba kudaden a masana’antar ta kanywood sadaka ce mai gudana da za a amfana ana duniya da gobe kiyama.
MOmo ya kuma yi kira ga mawadata da su dinka tallafawa masana’antar ta Kannywood da kudade kamar yadda suke tallafawa marayu da sauran masu bukata ta musamman.

Aminiya suma sun wallafa wannan hoto a shafinsu na twitter

Momo ya ce al’umma za su iya zabar irin fina-finan da suke so ayi musu da suka shafi al’ada da dabi’un malam bahaushe matukar za su dinga bada tallafin kudade ga masana’antar.
Ya kuma ce ya cancanta a rinka fitar da kudade daga cikin tsarin zakka da za a rinka shirya fina-finan hausa da sauran shirye-shirye domin jama’a su amfana.
Ya ce duk wanda ya zuba kudinsa a harkar fim tamkar yayi sadakatul jariya ne don kuwa ladan zai bishi har zuwa kabarinsa matukar za a dauka a kalla to zai samu lada a cewar sa.
Ya kara da cewa ko a baya anyi gwamnatotcin da suka bada kudade wanda aka shirya fina-finai kanana ta karkashin hukuma don tattare fina-finan da basu da kyau.
“Yana da kyau a dawo da wannan tsarin gwamnati da al’umma su fito da wadannan kudade.
“A nemi masu shirya fina finai ai tayi ana tura su kafofin sadarwa don toshe irin wandancan marasa kyau.
“Mun ga yadda ake tura wa’azuzzukan malamai kuma wasu suna fadakarwa, to idan aka dauki wannan salon aka rinka shirya wadannan fina-finan to za su taimaka matuka,” a cewar sa.
Ya kara da cewa yakamata a dunga yiwa al’umma kyakkyawar fahimta ta yadda za a samu gyara ya ce akwai nauyi akan attajiran mu da su rinka fitar da zakkarsu ga masana’antar shirya fina finan hausa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

4 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button