Labarai

Ba Na Son Komawa Wajen Iyaye Na Na Fi Son In Koma Inda Na Fito

Advertisment

Wannan yarinyar sunanta Nusaiba Jibril, shekarunta 16, sunan mahaifiyar ta Sha’awa daga ‘Yar Dorawa Samaru Zaria a Jahar Kaduna.

Shugaban babajo Foundation

‘Yan JTF suka tsinceta tana gararanba akan titi a ranar Larabar da ta gabata, ganin cewa yarinya ce kuma mace sai suka dauketa izuwa ofishinsu dake Barnawa Layin Hakimi a Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, bayan sun bata abinci taci ta koshi sannan sukai mata tambayoyi daga bisani suka kira Haj. Sadiya Isa Suleiman (Babajo Foundation) don samun mafita.
Nusaiba ta shaidawa AmaleHausa24 cewa “ina aiki ne a Gidan wata mata mai suna Maimuna a Shagari Low cost dake Barnawa Kaduna”
“Wata na hudu da sati biyu ina aiki a gidan, ana azabtar dani sosai musamman wata tsohowa a Gidan da ake kiranta Hajiya, ta kore ni a Gidan ne saboda wai banyi shara da goge-goge ba na rana daya kawai, kuma wallahi nayi shine tace sai na tattara kayana na bar mata Gidan”
Sai dai Nusaiba tace ita fa bazata koma Gidan Iyayen ta ba, don ko ta koma ma bata da wurin zama tunda babanta sun rabo da maman, hasalima Baban bai san halinda take cikiba.
Nusaiba tace mata biyu Babanta keda su kuma tana da kanne akalla 7, Baban magini ne a Abuja dan takamaimai ma bata san inda yake yanzun ba.
Nusaiba ta roki Babajo Foundation da su nema mata ‘Yancin ta ta yadda zata samu ‘Yanci mai dorewa, saboda idan mamanta taji har takai karar wacce take aiki a wajenta to ta shiga uku.
An samu kayan sawa da kayan kwalliya da kwayoyi da takardar shaidar saka kudi a banki da sauran tarkace acikin jakarta.
Aikaita Unguwan da tace tana aikin amma bata gane Gidan ba.
Yarinyar bata jin dadin jikinta, kuma alamu na nuna kamar tana dauke da juna biyu.
Kwamared Abubakar Yahya Ibrahim

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button