AUDIO + VIDEO : Zama Na Musamman A madadin Tafsir Akan Tabargazar Abduljabar ~ Dr Sani Umar R/lemo
*ZAMA NA MUSAMMAN A MADADIN TAFSIR*
*TONON SILILI GA ABDULJABBAR NASIR KABARA*
DR.MUHD SANI UMAR R/LEMO (HAFIZAHULLAH)
*WASU DAGA CIKIN BAYANAN DA ZAMAN YA KUNSA:*
(1) Nuni zuwa ga Tarihin masu mummunar akida da irin yadda karshensu ya kasance.
(2) Girman sharri da illar masu sanya rigar addini amma su na yi wa addinin zagon kasa.
(3) Duk wanda ya rushe Hadisai kawai ya rushe Hukunce-Hukuncen Shari’ar Musulunci ne.
(4) Ta ya ya makiya addini ke rusa Hadisai?
(5) Ina Akidar rushe Hadisai ta samo asali?
(6) Rubucen-Rubucen da Malamai suka yi domin bayanin munanan akidu.
(7) Tonon Silili ga Abduljabbar Nasiru Kabara da takaitaccen tarihin yadda barnarsa ta faro.
(8) Shin Abduljabbar Nasir Kabara yana wani bincike na ilimi?
(9) Su waye iyayen gidan Abduljabbar Nasir Kabara? Da su wa ya dogara?
(10) Bayan sanya Abduljabbar Nasir Kabara takunkumin magana me kuma ya kamata ya biyo baya?
22/6/1442 – 5/2/2021
Wannan wajen da anka rubuta ‘download mp3 ‘ nan zaku latsa domin Downloading.
https://youtu.be/xKrvggnlsPM