Labarai
An miƙa wa Ganduje rahoton muƙabala da Sheikh Abduljabbar
Kwamitin da gwamantin Kano ta kafa kan yadda za a gudanar da muɓabala da Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da wasu malaman ya mika rahotonsa gaban gammana Abdullahi Umar Ganduje.
Kamar yadda bbchausa na ruwaito.Kwamishinan harkokin addini a jahar Malam Muhammad Tahar Adam da aka fi sani da Baba Imposible ya ce cikin buƙatun da kwamitin ya gabatar wagwamanan jahar sunhaɗa da gayyato manyan malaman da ake da su a kasar daga ɓangaren Izala da Tijjaniya da Ƙadiriya tare da wakilci daga fadar sarkin Musulmi.
Amma kuma Baba Impossible ya ce har yanzu gwamanatin jahar bata tsayar da ranar da zaa gudanar da muƙabalar ba.