Labarai

An Kama Wani Mutum Da Yayi Yunkurin Binne Matarsa Da Ranta Bayan Ya Gano Tana Dauke Da Cikin Abokinshi

Hoto daga Hutudole

An kama wani mutum dan shekaru 49 mai suna, Phillip Tersso, yayin da yake kokarin binne matarsa mai suna Mary da ya shafe shekaru 10 tare da ita, bayan ya gano cewa tana dauke da juna biyun abokinsa mai suna, Aondowase Chiahemba. Hutudole ta ruwaito
Tersso, dan asalin garin Yelwata ne dake jihar Nasarawa, ya hadu da matarsa Mary, shekaru 12 da suka gabata kuma ya aure ta bayan shekaru biyu.
Sun rayu cikin farin ciki a matsayin ma’aurata amma suna fama da matsalar rashin haihuwa saboda kusan shekaru 10 da aurensu amma basu samu rabo ba.

 
 

Tersso duk da haka ya yi fama da rashin lafiya kuma an kai shi asibitoci daban-daban domin yi masa magani.
 
Yana a kan gadon jinya, matarsa, Mary ta sanar da shi cewa za ta yi aure idan ya mutu kuma ta bayyana masa cewa tana dauke da juna biyun wani mutum, wanda ta bayyana shi amatsayi abokinsa.
A cikin fushin bayan matarsa ta gayamasa cewa ta sadu da wani mutum wanda ya kasance abokinsa, Tersso bayan ya murmure, ya kammala shirin kashe Mary da kuma kansa.

Ya kara da cewa wannan abun ya matukar saka shi cikin damu, shi yasa ya yanke hukuncin binne ta da ranta domin taji irin yadda yaji
 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button