Uncategorized

Abinda Yasa CBN Ya Haramta Amfani da kudin Internet A Nigeria

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umarci bankunan ƙasar da su rufe asusun ‘yan kasuwa da kamfanoni masu amfani da kuɗin intanet na cryptocurrency, matakin da bai yi wa dubban ‘yan ƙasar daɗi ba.

Kamar yadda bbchausa na ruwaito,Umarnin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a ga bankunan hada-hadar kuɗi (DMB) da kamfanonin da ba na harkar kuɗi ba (NBFI) da kuma sauran ma’aikatun harkokin kuɗi.

“Ƙari a kan umarnin da aka bayar tun a baya, bankin (CBN) yana tunatar da ma’aikatun da ke mu’amala da kuɗaɗen intanet ko kuma dillalansu cewa haramun ne,” a cewar sanarwar.

A shekarar 2017, CBN ya ce kuɗaɗen intanet irin su bitcoin da litecoin da sauransu ana amfani da su ne wurin ɗaukar nauyin ta’addanci da kuma halasta kuɗin haramun, ganin cewa ba a iya bin sawunsu.

“Saboda haka, an umarci dukkanin NBFIs da NBFIs da OFIs da su tantance mutanen da ke amfani da irin waɗannan kuɗaɗe sannan su rufe asusun ajiyarsu,” a cewar umarnin.

Kazalika a 2018, CBN ya ce kuɗaɗen ba sa cikin abubuwan da mai su zai iya kai ƙara kotu idan yana neman haƙƙinsa a Najeriya.

Takardar umarni daga CBN

Jerin kuɗin intanet da ake kasuwanci da su

  • Bitcoin
  • Ethereum (ETH)
  • Litecoin (LTC)
  • Cardano (ADA)
  • Polkadot (DOT)
  • Bitcoin Cash (BCH)
  • Stellar (XLM)
  • Chainlink
  • Binance Coin (BNB)

‘Yan Najeriya sun fusata

Fitar sanarwar ke da wuya, sai dubban ‘yan Najeriya suka fantsama shafukan zumunta domin bayyana ra’ayoyinsu, mafi yawa cikin fushi.

Wani mai suna @WhiteSammy_ a Twitter ya ce: “Kudin intanet ne alƙibla a nan gaba ko CBN yana so ko ba ya so. Dole ne mu yi nasara.”

 

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1

Shi kuwa Mark Amaza (@amasonic) alaƙanta abin ya yi da siyasa, yana mai cewa “na fuskanci wannan haramcin ba zai rasa nasaba da zanga-zangar #EndSARS ba”.

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 2

Tomiwa Gorilla (@thetommyk_) dariya ya yi kuma ya ce: “Jiya-jiyan nan na sauke manhajar kasuwancin kuɗin intanet amma kuma CBN yana faɗar wani abu daban???”

 

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 3

Kasuwanci da kuɗin intanet

Miliyoyin mutane a faɗin duniya na amfani da manhajoji iri-iri da ke ba su damar yin kasuwanci ta intanet ba tare da ɗaukar ruwan kuɗi ba ko kuma tura kuɗin da suka ajiye a asusun ajiyarsu na banki.

Sukan sayi abubuwan amfani daga wasu kamfanoni da suka amince a biya su da kuɗin intanet, kuma suna biyan kuɗin ne ta asusun wayar hannu ta salula.

Akwai manyan attajiran duniya da ke amfani da kuɗin intanet irin Elon Musk, wanda shi ne mafi arziki a duniya a yanzu.

A farkon watan Fabarairun nan ne attajirin ya ce “Bitcoin abu ne mai kyau” har ma ya yi nadamar rashin fara amfani da shi tun shekara takwas da suka gabata.

Wannan yabo da Musk ya yi wa kuɗin ce ta sa darajar Bitcoin ta kai dala 34,500 kafin daga bisani ta ragu. A watan Janairu, darajar tasa ta kai har dala 38,000 bayan Musk ya sauya sunansa zuwa #bitcoin a shafinsa na Twitter.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button