Labarai

Abduljabbar Kabara Bai San Abin Da Yake Yi Ba. Cewar Malamin Shi’a Hamza Lawal

Shahararren Malamin Shi’a a Najeriya Malam Hamza Lawal ya bayyana Abduljabbar Kabara a matsayin wanda ya ‘bata kuma ya ke ‘batar wa.
Abduljabbar Kabara wani mutum ne wanda bai san abin da yake yi ba a addinin musulunci. Ya na so ya sami kafuwa saboda haka sai yake cin karo da wasu abubuwa na ilmi, kasancewarsa ba shi da Malami sai ya zamo shi da kansa ne yake fitar da abubuwan da yake yi na martani.” Inji Hamza Lawal.
Kuma ya ce” Abduljabbar Kabara mutum ne wanda yake a gayar rudu, saboda ba shi da wanda zai shiryar da shi a kan abubuwan da yake yi. Abubuwan da yake yi wahamomi ne da zuciyarsa ke raya masa, sai ya zama yana fassara su a kan abin da zuciyarsa ke raya masa. Fassarar tasa ce jahilai ke cewa ilmi, irin wadannan mutane su ne ke ‘bata su ‘batar.”
DAGA Indabawa Aliyu Imam

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button