Zulum Yaji Dadin Naɗin sababbin Hafsoshin Tsaro
Mai Girma Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi maraba da nadin sabbin shugabannin hafsoshin, yayin da ya ke mika godiyarsa ga shugabannin hafsoshin da ke barin gado, musamman shugabannin sojoji kasa da na sama, Laftanar Janar Tukur Buratai da Air Marshall Abubakar Sadique wadanda gwamnatin Borno ta fi aiki da su a yaki da Boko Haram.
Zulum cikin takatacen jawabi a daren jiya Talata a Maiduguri, lokacin da wasu ‘yan jarida suka nemi jin ta bakin sa. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar a ranar Talata da rana, cewa ya amince da murabus din shugabannin sa (yanzu masu ritaya), kuma ya nada Manjo Janar Leo Irabor a matsayin shugaban hafsan tsaro, Manjo Janar Ibrahim Attahiru a matsayin shugaban hafsan sojojin, Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo a matsayin shugaban hafsan sojojin ruwa da Air Vice Marshal Isiaka Oladayo Amao a matsayin shugaban hafsan sojojin sama.
“Shugabanninmasu barin gado sun kasance tare da mu a cikin shekaru shida da suka gabata, kuma a cikin wadannan shekarun da suka faru da kuma kalubale, sun ba da gudummawa matuka ga ci gaba da kokarin samar da zaman lafiya ta hanyar yaki da Boko Haram, kuma sun taimaka matuka a sauran kokarin ci gaban.
A kokarin mu na sake ginawa da sake tsugunar da yan gudun hijira yana samun Nasarane saboda kokarin da Laftanar Janar Buratai ya yi a matsayin shugaban hafsan sojan,da Air Marshall Sadique a matsayin shugaban hafsan sojojin sama, tabbas tare da gudummawa da yawa daga sauran shugabannin hafsoshin, hukumomin leƙen asirin, ‘yan sanda, jami’an tsaro da kuma masu sa kai Ba za mu iya yin watsi da waɗannan manyan gudummawar ba, amma fa, kamar yadda dukkanmu muka sani, komai yana da lokacin da aka tsara, muna gode wa shugabannin sabis masu barin gado saboda gudummawar da suka bayar kuma muna musu fatan alheri a ayyukan da za su yi a nan gaba.
Game da sabbin, musamman, Janar Leo Irabor wanda shi ne babban hafsan hafsoshin tsaro da Janar Attahiru, COAS, dukkansu sun yi aiki a nan Borno a matsayin kwamandojin aikin Lafiya Dole, sun san dukkan batutuwan kuma na tabbata su zai buga kasa a guje.
Gwamnatin Jihar Borno za ta ba su hadin kai kamar yadda taba wa magabatan su, kuma za mu ci gaba da taka rawar mu wajen tallafawa sojoji da kayan aiki kamar yadda muke yi a kai a kai, za mu ci gaba da hada kan al’umma don tattara bayanan sirri,da ayyukan dubban masu aikin sa kai, suna yi wa sojojinmu da masu sa kai addu’o’i a layuka tare da tallafa wa iyalansu kamar yadda muke yi ”cewar Gwanma Zulum
Voice of Borno…………