Labarai
Yanzu-Yanzu:A halin Yanzu ana musayar wuta tsakanin Boko Haram da Sojojin Najeriya a Borno
Rahotannin dake fitowa daga jihar Borno na cewa a halin da ake ciki yanzu sojojin Najeriya da Mayakan Boko Haram na musayar wuta a kauyen Kurmari dake tsakanin Maiduguri zuwa Magumeri.
Da Misalin karfe 12:10 na yammacin yau ne aka fara bata kashin kamar yanda Eonsintelligence ta ruwaito.
Hutudole na ruwaito wannan labari, dama dai an samu bayanan Sirri cewa Boko Haram zata tsananta kai hare-hare bayan nadin sabbin shuwagabannin tsaro da shugaba Buhari yayi, dan ta nuna cewa har yanzu tana nan da karfinta