Labarai

Yadda matashi ya yi garkuwa da mahaifinsa ya karbi naira miliyan 2 kuɗin fansa

Rundunar yan sandan Najeriya, ta cafke wani dan shekara 20, Abubakar Amodu, bisa shirya tawaga don garkuwa da mahaifin sa tare da karbar kudin fansar miliyan biyu, The Nation ta ruwaito.
Amodu na daya daga cikin masu laifi 25 da kakakin rundunar yan sanda, CP Frank Mba, ya kama da laifuka daban daban a Abuja.
An kama wanda ake zargin, tare da wasu yan tawagar sa, ya ce yana aiki da mahaifinsa suna aikin kiwo a gona. A cewar sa, baban nasa ya bashi shanu 15 kuma ya bar gidan. Ya ce ya kulla abota da abokan tawagar tasa, wanda suka shaida masa mahaifin sa mai kudi ne, ya kamata ayi garkuwa da shi a samu kudi.
 
 
 
Ya amsa hada tawaga da tayi nasarar sace mahaifin nasa kuma ya samu naira 200,000 a cikin kudin. Kakakin yan sanda, CP Frank Mba ya ce lokaci ya yi da rundunar za ta daina ragawa yan ta’adda.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button