Labarai

wata sabuwa| Babu Wanda Ya Isa Ya Tsaida Mana Wani Yaro A Matsayin Dan Takarar Gwamna A Jahar Sokoto A Zaben 2023 ~ Dr Salame

Dan majalisar tarayya mai wakiltar Gwadabawa da Illela a jam’iyyar APC Hon. Abdullahi Balarabe Salame ya bayyana cewa daga yanzu sun shirya tsaf domin yin fito-na-fito da wani azzalumin mutun wanda yake amfani da rigarsa yana cutarda magoya bayansa.
Dr Salame ya ce daga yanzu baza su kara bari wani mutun wanda yake bai girme su da wasu shekaru ba yana juya su yadda yaga dama ba. Saboda haka sun shirya tsaf domin yin fada da wannan azzalumin mutun.
 
 
 
Salame ya bayyana cewa, akwai ban haushi irin yadda wannan mutun yake yin abubuwan da yaga dama wajen tsayarda dan takara, inda yake shiga cikin gida shi kadai ya yanke shawara batareda ya tuntubi magoya bayansa ba.
Dr Salame ya ce su kam daga yanzu zasu fara fada da wannan mutun don ganin sun koya masa darasi.
Mutane da dama ne dai ke ganin cewa wadannan kalamai na Salame ya yi su ne zuwa jagoran jam’iyyar APC a jahar Sokoto Sanata Dr Aliyu Magatakarda Wamakko.
Tushen labari : Nasara

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button