Labarai

Ubangiji Allah Ya Ruguza Gwamnatin Faransa Da Magoya Bayan Ta Sun Rufe Masallatai 9

A yau Majiyarmu ta samu wani mummunan labari daga shafin nasara wanda sunka wallafa wani labari mai muni ga abinda suke cewa.
Gwamnatin kasar Faransa karkashin jagorancin Emmanuel Macron na ci gaba da takurawa al’ummar musulmi na wannan kasa ba dare ba rana.
Yanzu haka dai gwamnatin kasar Faransa ta rufe masallatai har 9 tareda hanawa ‘yan uwan mu musulmai kusanto wadannan masallatai domin bautar Allah.
Wannan dai yana faruwa ne saboda ‘yan uwan mu musulmai sun nuna takaicinsu akan cin zarafin fiyayyen halitta da jaridar Chalier Hibdo take yi na zanen fiyayyen halitta.
Yanzu haka dai babban bakin cikin kasar Faransa da kasashen musulmai shine; Kusan dukkanin kasashen musulmai na duniya sun daina sayen komai na kasar Faransa, wannan ya yi matukar yin sanadiyyar rugujewar tattalin arzikinta mai tarin yawa a karshen shekarar 2020 da kuma farko-farkon wannan shekara ta 2021.
Kuma muna rokon Allah madaukakin sarki ya ci gaba da ruguje tattalin arzikin wannan kasa har izuwa lokacin da suka daina goyon bayan cin zarafin fiyayyen halitta.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button