Kannywood

Soshiyal midiya ta kashe kasuwancin waƙoƙin Hausa ~ Adamu Hassan Nagudu

ADAMU Hassan Nagudu ya na cikin sahun farko na mawaƙan Hausa na zamani. Ya shafe shekara ashirin ana damawa da shi a Kannywood, inda ya ciri tuta da daɗaɗan waƙoƙi, masu ma’ana, waɗanda ke jefa duk mai sauraro cikin kogin tunani. Adamu ya samu farin jini irin wanda ba ya misaltuwa.
Daga baya kuma sai mawaƙin ya koma ɓangaren fitowa a fim a matsayin jarumi. A nan ma ya ciri tuta, duk da yake ba kamar a fagen waƙar ba.
To kuma sai aka ji shi shiru a ɓangaren waƙar, domin kuwa yanzu ya kai shekara biyu ba a ji ya yi sabuwa ba. Don haka mutane ke tambayar shin me ya faru ga Adamu Nagudu ne? Shin Nagudu ya gudu ne? Ko karyewar kasuwar finafinai ce ta kore shi daga fagen?
Waɗannan tambayoyin su ne su ka sa mujallar Fim ta tunkari Nagudu domin ya amsa mana su. To, ashe dai an sosa masa inda ya ke masa ƙaiƙayi, don haka mun tattauna da shi inda ya amsa mana dukkan tambayoyin, har ma da wasu, kamar haka:
FIM: Da farko, ina Adamu Hassan Nagudu ya shiga tsawon lokaci?
ADAMU NAGUDU: Assalamu alaikum. Mai magana Alhaji Adamu Hassan Nagudu. To, Adamu Nagudu ya na nan bai gudu ba kamar yadda wasu ke  faɗin cewa “Nagudu ya gudu!” Ina nan a tsaye in-sha Allahu.
FIM: A wane mataki Adamu Nagudu ya ke a yanzu a harkar waƙe-waƙe?
NAGUDU: A harkar waƙe-waƙe Adamu Nagudu na nan a matsayin sa na mawaƙi kuma jarumi kamar yadda kowa ya sani, sananne, tsoho ba sabo ba.
FIM: Akwai mawaƙa da dama da ku ka yi tashe tare da su a zamanin ku, yanzu kuma ba a jin su, wasu ma an manta da waƙoƙin su, amma kai sai ga shi har yanzu idan ka yi sabuwar waƙa masoyan ka na wasoson ta. Menene sirrin?
NAGUDU: Abu ɗaya zan iya faɗi a kan wannan tambayar da ka yi min. Ita waƙa adabi ce, sannan kuma siga ce. Kowane mawaƙi ya na da sigar da ya ke waƙar sa, kuma ya na da sagigar salon yadda ya ke tafiya da salon waƙoƙin sa. Sannan kowane mawaƙi ya na da salon sigar da masoyan sa ke bibiyar sa. Don haka ba zan iya cewa na fi wani ba ko na fi kowa ba. Ni dai abin da na sani idan zan yi waƙa ko da na daɗe ban yi ba na kan zauna in natsu in maida hankali na wuri guda, in kalla a zamanin me ke tafiya, waɗanne irin kalmomi ne ke tafiya, wane irin kiɗa ke tafiya, wane yanayi wanda masoya su ke kallo a wannan lokacin? Na kan ɗan ƙoƙarta in yi daidai da zamani da kuma abin da masoya ke buƙata. Ina ganin dalilin wannan tafiya da na ke yi da zamani shi ya sa masoya ke bibiyar al’amura na har yanzu.
FIM: An ɗauki tsawon lokaci ba ka saki sabon album ba kamar yadda ka saba. Menene dalili?
NAGUDU: Haka ne, tunda yanzu za a kai tsawon shekara uku a taƙaice ba a ga sababbin waƙoƙi na na ji da na kallo ba. Na yi sababbin waƙoƙi na ji da na kallo, amma saɓanin yadda ta juya, ba zan ce kasuwa irin tamu ta fim ba, kasuwanci na duniya baki ɗaya kowa ya san ya juya. Ni a gani na duk wanda ya san harkar kasuwanci ya damu da ƙima, ba riba ba. Saboda haka duk lokacin da ka yi wani abu ka san cewa ba fita za ka yi ba, to za ka bi yadda wannan saƙon naka zai isa ga waɗanda ka yi domin su. In ka lura yanzu harkoki sun koma soshiyal midiya, kasuwar babu ita, ko da ka kai ma sai dai ka samu faɗuwa, ba riba. Saboda haka dole masoya su yi mana haƙuri, domin ka zuba kuɗin ka ka yi shutin, ka yi waƙoƙi da sauran su, ka je ka kai kuma ba ka ƙaru da komai ba, ka ga abin babu daɗi. Saboda haka mu na bin abin yadda saƙonin mu za su isa ga masoyan mu, mu ma mu samu, kuma su samu cikin sauƙi, wannan hanya kuwa ita ce hanyar midiya.
A yanzu idan ka je kasuwa ba za ka samu waƙoƙin mu ba, amma ka na hawa YouTube za ka samu waƙoƙin mu. Kamar ni yanzu, da ka shiga ka rubuta “Adamu Nagudu TV” za ka samu waƙoƙi na sababbin duk irin wanda ka ke so. Saboda yanzu kasuwar ta koma can.
FIM: Amma kuma ku na samun kuɗi a YouTube ɗin kamar yadda ku ke samu a kasuwa a baya?
NAGUDU: Gaskiya ba a samun wani abu kamar yadda ake samu a baya. Amma dai  shi zamani ya na tafiya ne da abin da ya zo da shi. Don haka idan ba ka tafi da wannan zamanin ba, gaskiya za a tafi a bar ka!
Saboda haka ‘benefit’ ɗin shi ne ka ci gabada ɗorawa, za ka samu riba fiye da abin da ka ke samu a kasuwa. Amma a cikin masoya in ka kasa su a cikin kashi ɗari ba kowa ya san yadda zai shiga YouTube ɗin ba ma, ‘yan ƙauye sai dai su shiga kasuwa su saya. Don haka mu na yi ne a hankali, a sannu masoyan mu za su fahimci inda kasuwancin namu ya koma, za su biyo mu, kuma za mu samu ribar mu kamar yadda mu ke nema, in-sha Allahu.
FIM: A can baya an san ka a matsayin mawaƙi, lokaci guda kuma aka ga ka rikiɗe ka zama jarumi, ka na fitowa a fim. Me za ka ce ya janyo haka?
NAGUDU: Gaskiya ba rikiɗewa na yi ba. Da ma tun can jarumi ne ni, waɗanda su ka san ni tun farkon farawa ta sun san ni a jarumi. Waɗanda su ka san ni a mawaƙi kuma sun san ni a mawaƙi, amma ainihi na jarumi ne ni, kuma da jarumta na soma, sai dai an ce ba a haɗa gudu da susun ɗuwawu. Na fara waƙa ne a yanayin da na tsinci kai na, kusan ita ce ɗaukaka ta, kuma ita ce hanyar da na ga Allah ya fi ba ni baiwa a kai. Ka ga dole zan fi bada hankali na a kai.
To, tunda kuma na samu abin da na ke so daidai gwargwado, sai na ɗan daɗa karkatowa a kan yadda aka san ni a kan harkar aktin ina taɓawa kamar yadda aka san ni.
FIM: Ka kai wane mataki a ɓangaren aktin ɗin?
NAGUDU: A ɓangaren aktin ban kai kowane mataki ba, ina nan a matakin farko a matsayi na na jarumi wanda ya fara, wannan shi ne.
FIM: Me za ka ce game da halin da masana’antar finafinai ta Kannywood ta shiga?
NAGUDU: Da ma a wannan lokacin duk wani mutum da ya ke cikin wannan masana’anta ta fim  da harkar waƙa ya san cewa wannan lokacin zai zo. Domin masana da masu hasashen kasuwanci da shi kan shi harkar fim ɗin su na haska mana tun a wancan lokacin. Akwai abubuwan da ake yi waɗanda ba su dace ba game da ‘yan kasuwar mu, furodusoshin mu da mu kan mu mawaƙan da ma jarumai masu fitowa a fim ɗin. Akwai wani tsari wanda an sauka a kan shi, a lokacin su na haska mana irin wannan haskawar, ba zan manta ba. Ana “a gyara kaza, abu kaza na iya lalacewa”. A wancan lokacin ba wanda ke kawowa cewa “kasuwar za ta juya, don haka zan samu matsala babba a wannan ɓangaren”.
Kasuwanci a yanzu ya lalace, ya juya fiye da yadda ka ke tunani, kaɗan su yi tunanin kasuwar za ta iya juyawa ta kuma lalace. Yanzu ba za ka iya cire naira miliyan ɗaya ba ka ce za ka zuba ka yi fim ka kai kasuwa ba, domin ka na tunanin in ka zuba su ta ina za su dawo, ba ma ka samu riba ba. To, ka ga duk abin da za ka yi babu riba ai barin sa shi ya fi.
FIM: Me ka ke ganin za a yi wanda za a samu mafita a kan wannan al’amari?
NAGUDU: To, sauyi guda ɗaya ne. A duk duniya baki ɗaya hangen masana’anta ta industiri ta duniya baki ɗaya, gwamnati ita ce mahangar ta. Abin da ya sa na kawo gwamnati, idan ka je Indiya akwai gwamnati a cikin industiri, haka Chana, haka Amerika, Ingila da sauran su. Su za ka ga gwamnati ta na tallafa masu da kuɗaɗe, gidaje, motoci da duk wasu abubuwa da ka san ana buƙata a harkar fim.
To mu a nan Arewa ma ba a yarda da harkar da ka ke yi ba ma ballantana a ba ka tallafi; ana kallon ka ɗan iska, ana kallon ka a mutumin banza, ana kallon ka a matsayin ɓatagari, ba a yarda sana’a ka ke yi ba. Saboda haka duk wani tallafi da ake badawa don a gyara sana’ar wallahi ba mu samu, kaɗan ne daga ciki wanda su ke iya fuskanta su taimaka da wani abu nasu waɗanda ake da buƙata, kamar su ofis, gidaje motoci ko wasu kuɗaɗe ma da ake tunani.
Amma tabbas da gwamnati za ta shigo harkar fim ta zuba kuɗin ta ta taimaka wa ‘yan fim  in-sha Allahu in aka samu haɗin kai a tsakani za a kai inda ba a tunani.
Don haka akwai ƙarancin sa hannun gwamnati, sannan  mu ma akwai ƙarancin fuskantar juna a tsakanin mu: ta ina ma za mu fara fuskantar gwamnatin, ta wace siga, ta wace hanya? Duk akwai ƙarancin waɗannan abubuwan. Shi ya sa za ka ga harkar kawai yau ta na gaba, gobe ta na baya.
FIM: Akwai wata hanya da ka ƙirƙira don fitar da waƙoƙin ka ga masoyan ka, musamman irin waɗanda ba su hawa soshiyal midiya, kuma su na buƙatar waƙoƙin ka, amma ba su san yadda za su yi su samu ba? Ka na da wata hanya da za su samu waƙoƙin ka cikin sauƙi?

Adamu Hassan Nagudu ya ce ya na tafiya ne tare da zamani

NAGUDU: Haka ne. Kamar yadda na faɗa maka a baya, na ce maka a kasuwanci ka damu da ƙima ba riba ba. Ina jin masoya na a cikin zuciya ta, kuma martabar su da ƙimar su ta nan yadda ta ke a zuciya ta. Ina nan ina ƙirƙirar wasu hanyoyi, sai wannan matsalar korona bairos ɗin da ta addabi duniya ita ce ta ɗan katse min hanzari na. Amma na gama shiryawa tsaf, a duk inda masoya na su ke zan yi tattaki in je gari-gari in ɗan haɗa gangami na ‘show’, in samu goyon bayan wasu mawaƙa ‘yan’uwa na waɗanda za su goya min baya don in tallata haja ta ta waɗannan waƙoƙi domin su kai ga masoya na, kamar irin su Ali Jita, Hussaini Danko, Umar M. Shareef, Ado Gwanja, da sauran dai mawaƙa ‘yan’uwa na. Mun gama shirin, kuma ya na nan bai canza ba. Mu na jira ne mu ga ƙasar ta gama saisaitawa mu shiga lungu da saƙo mu raba kayan ma kyauta.
Na san akwai waɗanda ba za su iya shiga intanet su samu ba, don haka sai ka je garuruwan su, duk inda mutum ɗaya ya samu, goma sun samu. Mu na nan mu na ƙoƙari, kuma in-sha Allahu za mu gabatar da wannan haja ga masoyan mu.
FIM: Ko Adamu Nagudu ya na yin irin wannan sabon salon da ake yi ka sayar wa wani waƙa ya je ya hau, musamman ƙananan jarumai? Wasu mawaƙan ma har kyauta su ke bada waƙoƙin su ga irin waɗannan jarumai. Wasu na ƙorafin cewa a kan haka irin waɗannan jaruman sun raina wasu mawaƙan da ke ba su waƙoƙi don su hau, su na masu wulaƙanci da cewa “ni ba zan hau waƙar wane ba”. Menene tsarin ka a kan haka?
NAGUDU: Gaskiya tsari na na san daɗin waƙa, na san darajar waƙa, kuma na san mecece waƙa daidai fahimta ta. Saboda haka ban ce idan yau jarumi ya zo ya na so ya sayi waƙa ta don ya je ya hau ko tsohuwa ko sabuwa ba zan iya bayarwa ba, a’a, gaskiya ba na bayarwa a yanzu, sai in na tabbatar da ingancin abin da za ka yi wa waƙar. Domin ba zan ɗauki waƙa ta da na ke tunanin na shirya ta tun daga tunani na ga abin da zan yi mata, ga abin da zan yi mata, sai kuma ya kasance kai in ba ka waƙa ka je ka yi yadda ka ga dama da ita ba, wanda in ka gama aka ce in kalle ta ba zan iya kallon ta ba.
Saboda haka, ni gaskiya ba na ɗaya daga cikin waɗanda ke bada waƙoƙin su ana yin irin waɗannan bidiyoyin. Sai na tantance, na yarda da wanda zai bada umarni da wanda zai hau waƙar sannan zan yarda in saida wa ko mace ko namiji, saboda akasari kashe waƙar ake yi ba gyarawa ba. Sai ya kasance kai ba zai ƙare ka da komai ba, daraktan ba zai ƙare shi da komai ba, shi wanda ya hau ba zai ƙare shi da komai ba.
FIM: Mecece shawarar ka ga abokan sana’ar ka?
NAGUDU: Alhamdu lillahi! Shawarar da na ke da ita, musamman ga mawaƙan mu na yanzu da na ke gani su ke tasowa sababbi, mun gode wa Allah mun yi iya abin da za  mu yi: shekara ɗai-ɗai shekara ashirin ka na abu ɗaya. Da a ce inda aka ci gaba ne, da yanzu mun naɗe hannu mun koma gefe guda ana yi mana fifita, mu na hutawa!
Duk da haka dai ba za mu ce ba mu huta ba, amma ba za mu huta da bakin mu ba.
Shawarar da zan ba su ita ce su ci gaba da jurewa, kuma su tantance abin da ya kamata su yi wajen kalaman su, abubuwan da ya kamata su furta, waƙa ko kiɗa, menene ya kamata in ɗauka in yi waƙa a kan sa, tunda kowa da irin waƙar da ya ke yi, wani fannin wa’azi, wani soyayya, da sauran su. To, akasari yanzu mawaƙan mu yaro da ya zo ya yi waƙa ɗaya, biyu, sai ya ga kamar shekara ashirin da ka yi ka na waƙa daidai ku ke. Don haka ina roƙon su da su bi a hankali; idan Allah ya yi za ka ɗaukaka, za ka ɗaukaka. Ɗaukaka  ba ta ƙarfi ba, ba da wayo ba, ba da dabara ba, sai ka yi waƙar ma ka na gida kwance Allah sai ya ɗaukaka maka ita ba ka taɓa tsammani ba. Saboda haka haƙuri, juriya da jajircewa su ne za su kai ka ga wannan mataki na ɗaukaka.
Kuma manyan mu waɗanda su ke sama da mu da mu da ke ƙasan, ina bada shawara duk inda ƙaramin mawaƙi ya zo a yi ƙoƙari a tallafe shi a taimaka masa da duk abin da ya ke buƙata, duk da yake wasu ba su duƙar da kan su don su na ganin sun kai, amma duk wanda ya zo da buƙatar taimako, kai babba ka taimaka masa. Wannan shi ne.
FIM: A ƙarshe, me za ka ce wa masoyan ka?
NAGUDU: Masoya na ina godiya ƙwarai da gaske domin ina ganin irin ƙaunar da ku ke nuna min ta kowane fanni da ɓangare. Ina godiya da addu’o’i da su ke yi min. Duk wasu abubuwa da ke faruwa tsakani na da su, sai dai in ce Allah ya saka da alheri.
FIM: Mun gode, Alhaji Adamu.
NAGUDU: Ni ma na godeMalam Abba.
Majiyarmu ta dauko muku wannan tattaunawa da Fimmagazine ta wallafa da tayi a shafinta.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button