Sana’ar Fim Ba Sana’a Ba Ce, Cewar ɗan’uwan ashiru na goma Da Ya Haukace
A wata tattaunawa da jaridar Dokin Ƙarfe TV ta yi da ɗan’uwan tsohon fitaccen darakta a masana’antar shirya fina-finan Hausa Ashir Na Goma, ya yi kira ga duk wasu shahararrun jarumai da mawaƙa na masana’antar ta Kannywood da ma masu sha’awar shiga harkar da su yi hattara domin harkar fim ba sana’a ce da za a yi alfahari da ita ba.
A dan haka ne ma ya gargaɗi duk ƴan cikinta da masu sha’awarta da su bi a hankali domin kafin su an yi ɗan’uwansa Ashir Na Goma wanda kafin rashin lafiya ta same shi ya samu duk wata dama ta kuɗaɗe da ganawa da shugaban ƙasa da sauran manyan mutane amma saboda ya samu matsalar jinya a yau, kowa ga guje shi. Babu wanda ya ke kula da shi sai iyayensa su kuma Allah ya musu rasuwa.
Idan ana biye da mu a jiya mun kawo hoton Ashir Na Goma cikin yanayi na ɗimuwa da rashin lafiya wanda hakan ya ja hankalin mutane da dama su ke cece ku ce akan yadda aka yi watsi da shi.
Majiyarmu ta dauko daga shafin dokin karfe.Sai dai kuma a tattaunawar da mu ka yi da shugaban hukumar tace- fina-finai Alhaji Na Abba Afakallah, ya musanta waɗannan bayanai na ɗan’uwan Nagoman sannan ya yi ƙarin haske akan lamarin.
Sannan kuma mun ji ta bakin manyan jarumai a masana’antar ta Kannywood, za mu kawo muku martanin da su ka mayar ta wannan shafi namu na Dokin Ƙarfe TV sai ku kasance da mu.