Labarai

Labari mai daɗi : Gwamnatin Tarayya ta bude sauran Iyakokin kasar

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da matakin cewa an buɗe dukkan iyakokin tudu na ƙasar, bayan sun shafe tsawon fiye da shekara ɗaya a rufe.
Cikin tsakiyar watan jiya ne Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da umarnin fara buɗe iyakoki guda huɗu, kafin yanzu a buɗe ɗaukacin iyakokin tudu da ke faɗin tarayyar Najeriya.
A watan Agustan 2019 ne Najeriyar ta rufe kan iyakokinta da nufin daƙile fasa-ƙwaurin musamman shinkafa da kuma makamai cikin ƙasar.
Babban kwanturolan Hukumar Shige da Fice ta ƙasar, Muhammad Babandede ya shaida wa BBC cewa tuni shugaban ƙasar ya ba da izinin a buɗe duka iyakokin ƙasar.
“Wannan ya yi dai-dai da lokacin da Najeriya ta shiga tarayyar ƙasashen Afirka kan tattalin arziki wanda za ta buɗe iyakarta don a yi kasuwanci kuma a yi zirga-zirgar mutane” in ji Babandede.
Ya ce da farko an buɗe iyakokin Seme da Maigatari da Illela da Nfom a ƙarshen watan Disambar bara.
“Dole ne mu tabbatar da cewa duka waɗanda za su shigo sun biyo ta ƙa’idar iyaka, sun bi da takardar izini kuma kada a tsangwami mutane na karɓar kuɗi wanda ba a yi shi kan ƙa’ida ba” a cewarsa.
Shugaban hukumar ya ƙara da cewa an tanadi ma’aikatan lafiya a kan iyakokin ƙasar da za su riƙa tabbatar da cewa mutane sun bi duka ƙa’idojin cutar korona.
A cewarsa, ma’aikatan za su duba mutane musamman yanayin zafin jikinsu sannan za su tabbatar da ana ba da tazara tare da sa takunkumi domin hana bazuwar cutar.
Ya ce hukuma ba za ta bari waɗanda suka karya ƙa’idojin su samu shigowa Najeriya ba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button