Labarai
Labarai da dumi-dumin su: Gwamnatin tarayya ta sanya ranar komawa makarantu
Gwamnatin Tarayya ta sanya ranar 18 ga Janairun nan a matsayin ranar komawa makarantu.
Ta ce ta dauki wannan mataki ne bayan cimma yarjejeniya da Gwamnoni, da Kwamishinoni da sauran masu ruwa da tsaki.
Majiyarmu ta samu labarin daga BBC An cimma matsayar ne a wata ganawa tsakanin Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu da Kwamishinonin Ilimi a Abuja.
Babban Sakatare a Ma’aikatar Ilimi ta tarayya Sonny Echono, wanda ya tabbatar da hakan ga THE NATION, ya ce:“Mun tattauna sosai tare da gwamnonin jihohi, da masu mallakar makarantu, da kungiyoyin kwadago da na ma’aikata da wakilan daliban.
Kuma yarjejeniya ita ce cewa ya kamata mu sake buɗe duk makarantu.